13 Afirilu 2021 - 12:37
​Iran: Zarif Ya Ce Shirin Nukliyar Kasar Iran Zai Ci Gaba Duk Tare Da Matsalolin Da Yake Fuskanta

Ministan harkokin wajen kasar Iran Mohammad Javad Zarif ya bayyana cewa shirin nukliyar kasar Iran zai ci gaba a dukkan cibiyoyin nukliyar kasar duk tare da harin da aka kaiwa cibiyar Natanz a jiya Lahadi.

ABNA24 : Kamfanin dillancin labarin IRNA na kasar Iran ya nakalto Abul Fadli Amuyi kakakin kwamitin tsaron kasa da kuma harkokin waje a majalisar dokokin kasar yana fadar haka a safiyar yau Litinin bayan ganawarsu da Mohammad Javad Zarif.

Ammuyi ya ce, ministan ya tabbatar masu cewa zasu bijiro da wannan batun a taron kasashen 4+1 na yarjejeniyar JCPOA wandada za’a gudanar a birnin Vienna a cikin ‘yan kwanaki masu zuwa.

Dangane da yarjejeniya mai dogon zango da kasar Sin kuma Zarif ya ce, kasar Sin za ta kasance babbatar kasa wacce zata sauya al-amura a duniya nan gaba, don haka samar da irin wannan yarjejeniya tsakaninta na Iran ya na da kyau.

Daga karshen ministan ya ce Iran tana kan matsayinta na cewa dole ne Amurka ta daukewa kasar takunkuman tattalin arzikin da ta dorawa kasar gaba daya kafin Iran koma aiwatar da yarjejeniyar JCPOA. Kuma babu tattaunawa da Amurkan kan wannan batun kai tsaye ko ta wakilci.

342/